Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kariya daga Bauta da kuma Aikin Dole, Ghana


Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays


Gabatarwa

Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org

Sahe na 16: Kariya daga Bauta da kuma Aikin Dole

  1. Babu wani mutumin da za a riƙe da bauta ko aikatau.
  2. Babu wani mutum da za a buƙaci ya yi aiki bisa tursasawa.
  3. Bisa manufar wannan sashe, “Aikin tursasawa” bai haɗa da:
    1. Dukkan wani aiki da aka buƙata sakamakon yanke hukunci ko umarnin kotu ba; ko
    2. Dukkan wani aiki da aka buƙaci wani horarren mai aikin ɗamara ko hidimtawa a matsayin aikinsa ko, a yanayin da mutumin da yake da ƙorafi game da hidimtawa a matsayinsa na ɗaya daga cikin Rundunar Askarawan Ghana, dukkan aikin da aka buƙaci wannan mutum a bisa doka ya aikata a madadin waccar hidimtawar; ko
    3. Dukkan aikin da aka buƙata a kodawane lokaci da Ghana ke cikin halin yaƙi ko a yanayin gaugawa ko wata annoba da ke barazana ga rayuwa da zaman lafiyar al’umma, har ta kai ga cewa buƙatar wannan aiki a bayyane take ƙarara a wannan halin da kowanne irin yanayi da zai iya afkuwa ko yake afkuwa a wannan lokacin bisa dalilan magance wannan yanayin ne; ko
    4. Dukkan wani aiki a hankalce, da aka buƙata a matsayin ɓangare na ayyukan da aka saba ko wasu wajibobin ‘yanƙasanci.

Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci
Haƙƙoƙi da ‘Yanci
‘Yancin Rayuwa
'Yancin Walwala
Girmama Ɗan'adam
Kariya Daga Bauta
Yancin Daidaito
Kaɗaikatar Gida
Adalcin Shari’a
Kariya Daga Ƙwace
Muhimman ‘Yanci

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub